Kungiyar kwallon kafa ta Super Eagle's dake tarayyar Najeriya ta samu damar haurawa mataki na 33, a duniya a jaddawalin da hukumar FIFA ta fitar a bangaren kasashen da su kayi kwazo a kwallon kafa da take fitarwa a duk karshen wata.
Hukumar kula da wasan kwallon kafa ta duniya FIFA ta bayyana sakamakon ne a ranar Alhamis 25 ga watan Yulin 2019, inda tace Najeriya ta samu haurawa sama daga matsayin da take daga mataki na 45, zuwa na 33 ne saboda da irin rawar da ta taka a gasar cin kofin nahiyar kasashen Afirka ta 2019, wanda aka kammala a kasar Masar, inda Najeriya ta kai zagaye na uku bayan ta doke Tunisiya daci 1-0.
Da wannan nasara da Super Eagle's ta samu a duniya yanzu haka itace a mataki na uku a kasashen Afirka inda take bayan Tunisiya, da kasar Senegal.
Facebook Forum