Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA, ta bayyana cewar, kungiyar kwallon kafa ta Najeriya Super Eagles ta samu matsawa zuwa mataki na 31 jerin kasashen da suka fi iya murza kwallo.
Rahoton wannan watan na Nuwamba ya tnuna yadda kungiyar ta kara matsawa da maki 4 a taburin kungiyoyin zakaru a duniya.
Cikin jerin sunayen da aka wallafa a shafin hukumar, Najeriya ta samu maki 1493 fiye da abin da ta samu a watan Oktona 1481.
Hakan kuwa ya taimakawa kungiyar zama a mataki na uku a jerin kasashen da ke nahiyar, inda take biye da kasar Senegal da Tunisia wadanda ke da maki 1555 da 1509.
Samun matsayin kuwa na zuwa ne biyo bayan nasarar da Najeriyar ta yi da ci 2-1 a karawarsu da ‘yan wasan Jamhuriyar Benin, da kuma 4-2 da kungiyar Lesotho a wasan zakaru na Afrika.
Facebook Forum