Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fara Harkar Fim Daga Tushe Na Da Muhimmanci - Prof. Umar


Farfesa Umar Faruk Jibrin
Farfesa Umar Faruk Jibrin

A yau shirin Nishadi ya yi babban kamu domin kuwa Farfesa Umar Faruk Jibrin, na tsangayar koyar da aikin jarida ta jami’ar Bayero ta Kano, ya hallarci zaunren DandalinVOA.

Farfesan ya bude wata makaranta ta koyar da aikin fina-finai sakamakon kalubalen saukar kasuwar fina-finai, game da fasahar da duniya ta ke kai akan fina-finai.

An bude makarantar ta Digital Film and Television Institute ne domin kawar da matsalolin masana'antar Kannywood, inda yake cewa matsalolin da suka danganci kasuwanci fina-finai da cimma yadda duniya ta kai a fina-finai.

Farfesan ya ce dalilin haka ne ya ga ya zama wajibi a koyar da Fim tun daga tushe, kuma a ilmance.

Farfesa Umar Faruk ya ce ita wannan makaranta kafin dalibi ya kammala ta, sai ya hada Fim.

Ya kuma ce makarantar ta dauki tsarin koyar da Fim ne a aikace, wanda wannan ita kadai ce hanyar da za ta koyar da darasin cikin saukin fahimta, inda wannan makaranta ta "Digital Film and Television Institude."

Ya kara cewa abokansu 'yan Kudu masu shirya fina-finai tuni suka yi wa sashen Arewa nisa, dalilin da ya sa a yanzu ake yunkurin bude cibiyoyin da zai koyar da fina-finai.

Ga cikakken rahoton wakiliyar DandalinVOA Baraka Bashir.

please wait

No media source currently available

0:00 0:05:50 0:00

Facebook Forum

Bidiyo

Saurari Dalilin Da Ya Sa Ummi Zeezee Ta Ce Tana So Ta Kashe Kanta A Hira Da Wakiliyar VOA Baraka Bashir
please wait

No media source currently available

0:00 0:06:39 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Saurari Bayanin Jarumar Kannywood, Nafeesa Abdullahi
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:24 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Bikin Yini Na Auren Zawarawa A Kano
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG