Ana dan ganin sauki a tsadar kaya a Najeriya. Amma fa, duk da wannan alama ta yiwuwar ‘yan Najeriya masu fama da tsadar rayuwa su dada samun sauki, faduwar darajar Naira, inda dala 1 kan kama daga naira 1,200 zuwa 1,600, da kuma ci gaba da tsadar mai, na tauye wannan dan saukin da aka samu, tare da barazanar maido da tsadar rayuwar baya.
A hirarsa da wakilin Sashin Turanci na Muryar Amurka a Abuja, Gibson Emeka, wani injiniya mai ‘ya’ya hudu, mai suna Michael Anthony ya ce har yanzu ya na fama da tsadar kayan masarufi duk da dan saukin da aka samu. Tsadar ta ragu daga kashi 33.40% a watan Yuli zuwa kashi 32.15% a watan Agusta.
Injiniya Michael ya ce, “A watan Yuli, na sayi buhun shinkafa naira 65,000, amma a yanzu da na ke magana da kai, kwanaki uku da su ka gabata, na sai buhun shinkafa naira 95,000 a wannan kasar…. Har yanzu ina kashe kudi mai yawa wajen sayen kayan abinci a kasuwa….farashin kaya na hauhawa, saboda hauhawar farashin mai.”
Ita ma, wata Blessing Ochuba, mai sayar da kayan abinci, a wata ‘yar maciya da ke wani gefen garin Abuja, ta ce “mutanen da ada kan sayi buhunan abinci, ayanzu rabi ma su ke saye. Ni kaina, ada, na kan yi sarin buhuna 10 na shinkafa, amma yanzu ba na iyawa.”
Dandalin Mu Tattauna