A lokacin da gwamnatin shugaba Buhari ta kafa kwamitin kawo sulhu tsakanin bangaren zartaswa da bangaren majalisa wasu 'yan Najeriya na kira a kai zuciya nesa don kare muradun dimokradiya.
Ministan cikin gida Janar Abdurahaman Dambazzau yace babu wani sabani mai tsanani da zai gagari sulhuntawa.
Yace duk maganganun da ake ji ra'ayoyi ne kawai. Yana mai cewa ba ra'ayoyin manyan dake bangarorin biyu ba ne. Yace cikin irin tafiyar da a keyi dole ne wata rana a samu rashin fahimta. Idan an zauna za'a nemi a gyara.
Tsohon shugaban kamfanin matatar mai dake Kaduna Injiniya Kailani Muhammad yace babu inda kundun tsarin mulkin kasar yace idan an gabatar da sunan mutum sai daya ko biyu kada asake gabatar dashi. A kan Ibrahim Magu yace idan da baya aiki tsakaninsa da Allah da sun bara tuntuni.
Ya cigaba da cewa kada su bari abun nan da 'yan Najeriya ke cewa wai sun ki Magu ne domin yana bincikar wasu daga cikinsu ya tabbata. Yace idan basy tabbatar dashi ba akwai hanyar kirawo 'yan majalisar su koma gidajensu a zabi wasu.
Adamu Malam Madalla na ganin babu dalilin fakewa da kin Ibrahim Magu wanda ya kai ga dakatar da Sanata Muhammad Ali Ndume. Ya kira 'yan Majalisar su sake tunane. Yace ya sha tabbatar wa 'yan Najeriya cewa barayin biro ba zasu bari tafiyar tayi nisa ba.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani.
Facebook Forum