A daidai lokacin da ake bukukuwan ranar ‘yan jarida ta duniya, sai ga kamfanin sada zumunta na Facebook, ya rufe shafin wasu mutane da yake ganin suna haddasa fitina da ire-iren kalamansu.
Shafin ya hana shugaban kungiyar kare hakokin bakaken Amurkawa ta Nation of Islam, Louis Farrakhan, da wani mai rajin kare hakkin bil’adama Alex Jones, da ma dai wasu da ke rubuce rubuce masu gauni yin amfani da shafin.
A jiya Alhamis ne kamfanin yace mutanen sun karya ka’idojin sa na rubutu, ya kuma ce “duk wani mutum ko kungiya da ke kira ko yin kalamai da suke na batanci ga wasu, ko zage zage da cin zarafin wasu, basu da matsugunni a shafin nasa” koda kuwa wacce irin akida gare su, a ta bakin mai magana da yawun kamfanin.
An kuma hana mutanen saka hotunan su ta kafar Instagram, duk da cewa kamfanin bai bayyana wasu daga cikin ire-iren kalaman da suke rubutawa a shafukan nasu ba.
Facebook Forum