A look at the best news photos of Europe migrant crisis.
Matsalar Bakin Haure a Turai

1
Sojoji da 'yan sandan kasar Macediniya na kokarin ganin ana bin ka'ida yayinda bakin haure ke shiga jirgin kasa kusa da birnin Gevgeliji.

2
'Yan gudun hijira da bakin haure na jira don tsallaka iyaka, daga garin Idomini na kasar Girka zuwa kudancin Macediniya.

3
Wani dan sanda ya bugi wani mutum a lokacin da ya ke kokarin tabbatar da oda, a lokacin da bakin haure ki jiran jirgin kasan da zai kai su sansaninsu na wucin gadi.

4
Wani dan gudun hijra ya runtuma da gudu bayan da ya shiga yankin kasar Hunagary ta hanyar tsallake shingen da aka kafa na wucin gadi a wajen iyakar kasashen Hungary da Serbiya.