A Ethiopia, ko Habasha, ambaliyar ruwa da kasar take fama da ita, tana biye ne da fari mai tsanani, rabon da ganin irinsa shekaru 50 baya. Tuni ambaliayar ta halaka mutane masu yawa, ta raba wasu dubban mutane da muhallansu.
Haka nan matsalolin tattalin arzikin da bala'o'in zasu haifar zasu yi tsanani, domin kashi 3 na al'umar kasar suna da dogaro ne kan noma.
Saboda haka, reshen hasashen yanayin tattalin arzikin duniya na asusun IMF, yake jin tattalin arzikin Habasha a bana, zai sami koma baya.
Wadannan matsaloli sun sa tattalin arzikin kasar ya bunkasa da kashi 4.5. Wannan alkaluma, kodashike ya dara galibin ci gaban da kasashe da suke kudu da hamadar sahara suke samu, duk da haka, koma baya ne ga kasar, wacce ci gaban tattalin arzikinta yake nunka haka nesa ba kusa ba.
Kungiyoyin agaji suna hangen cewa idan aka ci gaba da ambaliyar ruwan, hakan zai raba mutane fiyeda dubu metan da muhallansu, kuma yayi nakasu ga rayuwar mutane dubu 485.