Mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, Enesto Valverde, ya bayyana cewa yanzu zai mai da hankalinsa ne kan gasar cin kofin zakarun turai wanda zasu fafata da kungiyar Liverpool a farkon makon na watan Mayu 2019.
Enesto ya ce duk da cewa har yanzu basu lashe gasar Laliga ba amma suna da kwarin guiwa akan cewa nan da sati daya gasar za ta tabbata a hannunsu da zarar sun doke kungiyar Levente.
Kungiyar Barcelona ta kara jin kamshin lashe kofin gasar La Liga ta Spain a bana, bayan da ta doke kungiyar Alaves da ci 2-0, bayan haka kuma tana wasan karshe na cin kofin Copa Del Rey wanda za ta buga da kungiyar Levente a karshen watan Mayu 2019,
Bayan haka kuma tana buga gasar cin kofin zakarun turai inda kawo yanzu taje matakin wasan kusa dana karshe kuma za ta fafata da kungiyar kwallon kafa ta Liverpool wadda ita ma take yunkurin lashe firimiyar kasar Ingila a bana.
Facebook Forum