‘Yan wasan Egypt sun cire Indomitable Lions na kasar Kamaru da ke karbar bakuncin gasar cin kofin kasashen nahiyar Afirka a gasar ta AFCON.
Hakan na nufin kasar ta Masar ta kai wasan karshe.
Egypt ta yi nasara ne da bugun fenariti da ci 3-1 bayan da aka kwashe minti 120 babu wanda ya zura kwallo.
Yanzu ‘yan wasan na Masar za su hadu da Senegal wacce tuni ta kai zagayen wasan karshe.
‘Yan wasan Kamaru sun zubar da fenariti uku a bugun daga kai sai mai tsaron gidan yayin da Egypt kuma ta ci duka wadanda ta buga.
Yanzu Kamaru za ta hadu da Burkina Faso don neman matsayi na uku a gasar ta AFCON wacce ake yi a karo 33.
Bangarorin biyu sun yi ta fafatawa cikin zagayen farko da kuma bayan an dawo daga hutun rabin lokaci, amma babu wanda ya kai ga gaci ta hanyar cin kwallo.
Wannan nasara ta Egypt na nufin fitattun ‘yan wasan Liverpool, wato Mohamed Salah da Sadio Mane za su hadu a wasan karshe wanda za a yi ranar Lahadi.