Kungiyar ci gaban kasashen Afrika ta yamma ECOWAS ta goyi bayan wacce Najeriya ta zaba domin takarar shugabancin hukumar da ke kula da kasuwancin duniya ta World Trade Organization.
Kungiyar ta kuma yi kira ga sauran kasashen Afirka da su goyi bayanta domin hada kan Afirka.
Najeriya ta zabi DR Ngozi Okonji-Iweala, wacce tsohuwar ministar kudi ce a kasar domin takarar mukamin.
"Muna kira ga gwamnatocin Afirka, da na sauran duniya da su goyi bayan Dr. Ngozi Okonjo-Iweala," a cewar shugaban kasar Jamhuriyar Nijar kuma shugaban kungiyar ta ECOWAS Mahamadou Issoufou a cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar.
Duk da cewar an sanya wa sanarwar kwanan watan ranar 19 ga watan Yuni, ba a fitar da ita ba sai yau, 22 ga watan Yuni.
Roberto Azevedo na Kasar Brazil shi ne shugaban hukumar a yanzu, kuma zai sauka a karshen watan Augusta mai zuwa.
A cewar mutane, ana matukar bukatar macce ta shugabanci hukumar tunda abu ne da ba a taba samu ba a can baya.
Magoya bayan Okonjo-Iweala wacce tsohuwar minista ce kuma babbar manajan babban bankin duniya, sun jadadda kwarewarta da kuma yadda ta samo wa Najeriya wasu kudaden (debt relief package) da suka kai yawan billiyoyin daloli.
A baya dai Afirka ta samu matsalolin hada kai wajen zaban wanda zai wakilce su a WTO.
Facebook Forum