Ministan harkokin wajen Britaniya Phillip Hammond, yace zuwa jiya Lahadi, kasar tana sa ran kimanin 'yan kasar dubu biyar ne zasu bar garin dake gabar teku. Duk da haka ofishin jakadancin Birtaniya dake Alkahira yana sannu-sannu na bayanin tururuwar da 'yan kasar suke yi na barin Masar.
Shugaban Rasha Vladimir Putin, makon jiya ya umarci gwamnatinsa ta dauki matakai na maido da 'yan kasar da suke ziyara a Masar. Mataimakain Firayim Ministan kasar Arkady Dvorkovich, ya fadi ranar Asabar cewa kimanin 'yan kasar Rasha dubu 80 ne suke ziyara a Masar, adadin da ya nunka abunda aka kiyasta tunda da farko. Jiya Lahadi wani jami'in kasar yace akalla 'yan kasar dubu 11,000 suka koma gida.
Fasinjoji 224, wadanda suka baro Sham el-Sheikh kan hanyarsu zuwa birnin St Petersburg suka halaka ranar 31 ga watan Oktoba, bayan da jirginya tarwatse a zirin Sinai na Masar.