Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dubban mutane suna ci gaba da halarta taron kasa da kasa akan kanjamau


Taron kasa da kasa akan kajamau a Washington DC
Taron kasa da kasa akan kajamau a Washington DC

Yanzu haka dubban mutane suna birnin Washington Dc nan suna halartar taron kasa da kasa akan kanjamau

Dubban mutane suna nan birnin washington DC a ranar ta hudu a taron kasa da kasa akan kanjamau da yake maida hankali akan munin cutar da yiwuwar jinyar cutar.

Jiya talata wani masani kimiya mai bincike daga kasar Spain mai suna Javier Martinez Picado ya fadawa mahalartar taron cewa, yanzu masanan kimiya masu bincike suna nazarin hanyoyin guda biyu na jinyar kanjamau.

Abu na farko shine kawar da kwayar cutar daga ciki mutane, ko kuma samun wata hanya ko kuma dabarar da jiki zata sarafa kwayar cutar a takaice jiki tayi watsi da kwayar cutar.

Haka kuma mataimakin sakatariyar harkokin wajen Amirka mai kula da harkokin kiwon lafiya mai suna Howard Koh yace Amirka tana fatar yawan masu kamuwa da kanjamau da wajen kashi ashirin da biyar daga cikin dari cikin shekaru uku masu zuwa.

A ranar ta uku da fara wannan taro masanan nan Amirka sun bada sanarwar wata sabuwar dabarar da aka tsara da nufin taimakon mata kare kansu daga harbuwa da kwayar cutar kanjamau ko SIDA.

XS
SM
MD
LG