Dubban maharba ne suka fito daga sassa daban daban na Najeriya don halartar babban taron al'ada na Salala da sukan yi duk sh'ekara.
Taron bana ya samu halarcin maharba daga kasashen ketare.
Da yake gabatar da jawabinsa a wajen taron saba layar, shugaban hadakar kungiyar maharba a shiyyar Arewa maso gabashin Najeriya, Alhaji Muhammadu Usman Tola, ya bukaci ‘ya’yan kungiyar ne da su hada kai da jami'an tsaro domin kwalliya ta biya kudin sabulu.
Kwamanda Philip Ngurore, dake zama kwamandan ‘yan Sakai daga jihar Yobe, daya daga cikin jihohin da bala'in Boko Haram ya fi shafa, yace taron tamkar an tashe su a barci ne.
Modibbo Idris Tola, shine sakataren tsare tsaren kungiyar kuma ya yi karin haske inda ya ce taron na bana ya sha banban dana shekarun baya. Suma mawakan maharba fa ba'a barsu a baya ba.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz da karin bayani
Facebook Forum