Bayanai sun tabbatar da cewa jami'an tsaro na DSS sun damke wasu mutane da ake tuhumar barayin daji ne, bayan dawowar su daga kasar Saudiya domin aikin hajjin wannan shekara.
Lamarin ya faru ne a filin jirgin saman sarkin musulmi Abubakar da ke Sakkwato, sa'adda jami'an tsaro suka yi dirar mikiya suka kama wasu barayi da suke tuhumar ‘yan bindiga ne.
Muryar Amurka ta zanta da wani jami'in tsaro da ke aiki a filin jirgin saman na Sarkin musulmi Abubakar da ke Sakkwato wanda bai da iznin magana a hukumance, amma dai ya sheda mana cewa a gaban idonsa lokacin yana kan aikin tarbo alhazzan jihar Zamfara, jami'an tsaro na DSS sun zo da jerin sunayen mutane kuma duk sun kama wadanda suke nema.
A cewar jami'in a cikin jirgin farko na alhazzan jihar ta Zamfara an kama mutum goma sha daya, a jirgi na biyu ma an kama mutum goma, dukansu maza.
Hakama wani rahoto, jaridar Premium Times ta ruwaito cewa an kama wasu alhazai bayan dawowar su daga makka, lokacin da suka sauka a filin jirgin saman Sarkin musulmi Abubakar dake Sakkwato.
A cewar jaridar wadanda aka kaman sun fito daga kananan hukumomin Tsafe, Zurmi, Bungudu da Shinkafi na jihar Zamfara.
Masu sharhi akan lamurran yau da kullum irin Farfesa Bello Badah na ganin cewa akwai darasi da ya kamata a lura da shi cikin wannan batun.
Lamarin rashin tsaro dai ya jima yana ci wa ‘yan Najeriya tuwo a kwarya inda suke ta kokawa akan mahukunta su kara kaimi wajen magance matsalolin.
Saurari rahoton a sauti:
Dandalin Mu Tattauna