Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

DOMIN IYALI: Yadda Matan Najeriya Zasu Tinkari Zaben 2023-Kashi Na Uku, Agusta, 25, 2022


Alheri Grace Abdu
Alheri Grace Abdu

Idan kuna biye da mu, shirin Domin Iyali ya karbi bakuncin wadansu ‘yan siyasa da su ka hada da mata da suka tsaya takara, wadanda ke nazarin yadda mata za su iya taimakawa ‘yan’uwansu da jam’iyunsu su ka tsayar takara, su iya kai ga nasara a zaben da ke tafe a Najeriya.

Bakin dai su ne. Hajiya Khadija Abdullahi Iya ‘yan takarar gwamnan jihar Naija ta jam’iyar AFGA, da Mrs Dorathy Nuhu Aken ‘Ova wadda ta nemi a tsaida ita takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyar SDP, sai kuma Hajiya Mariya Ibrahim Baba ‘yar siyasa kuma ‘yar gwaggwarmaya, da kuma dan siyasa Sa’idu Gombe.

Hon Sa’idu Gombe na bayanin kan inda yake ganin rauni a siyasar mata lokaci ya kwace mana, inda kuma mu ka dora ke nan yau a tattaunawar da Shamsiya Hamza Ibrahim ta jagoranta:

Saurari cikakken shirin cikin sauti:

DOMIN IYALI: Yadda Matan Najeriya Zasu Tinkari Zaben 2023-Kashi Na Uku
please wait

No media source currently available

0:00 0:10:07 0:00

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

XS
SM
MD
LG