WASHINGTON, DC —
A yau shirin Domin Iyali ya fara nazarin batun ahuwa da gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje ya yiwa Rahama Hussaini wadda tun daga lokacin da aka yi mata aure tana da shekaru 13 zuwa yanzu, ake muhawara a kan halin da ta shiga.
Shirin ya gayyaci masu ruwa da tsaki domin nazarin darasin da za a iya koya daga lamarin.
Saurari tattaunawa da wakilinmu Mahmud Ibrahim Kwari ya jagoranta:
-
Grace Alheri Abdu
Grace Alheri Abdu babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.