Ga wadanda suke sauraron wannan shirin karon farko yau, shirin Domin Iyali yana nazari ne kan yadda za a shawo kan cin zarafi da tashin hankali a tsakanin iyali da ake yawan fuskanta a kwanakin nan.
Shirin ya karbi bakuncin Alh Bello Sheriff, Shugaban Kungiyar matasan Najeriya reshen jihar Naija, da Mohammed Sa'idu Etsu, shugaban kungiyar inganta rayuwar matasa a jihar Naija, da kuma Barista Hadiza Nura Alfa, Lauya da ke kungiyar hake hakkokin mata WRAPA a jihar Naija.
Saurari cikakken tattaunawar da Mustapha Nasiru Batsari ya jagoranta:
-
Grace Alheri Abdu
Grace Alheri Abdu babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.