Wannan kiran na zuwa ne a cikin kasa da sa’o’i 48 da labarin kisan wata mata mai juna biyu da ‘ya’yanta hudu baya ga wasu direbobi biyu, masu sayar da tsire da ya kai adadin mutanen da aka kashe a yankin 12.
A ranar talata ne dai lamarin yadda wasu ‘yan bindiga da ba’a san ko su wanene ba suka kashe wata mata mai juna biyu da ‘ya’yanta hudu tare da wasu mutane 8 a jihar Anambra ya dada yaduwa a kafaffen sada zumunta inda ‘yan Najeriya musamman ma daga arewaci suka fara neman gwamnati ta nemawa mutanen da lamarin ya rutsa da su hakokkinsu cikin gaggawa.
Shugaban kwamitin amintattu na gamayyar kungiyoyin arewa, Alh. Nastura Ashir Sahriff, ya bayyana cewa wannan alamari ba sabon abu bane ya na mai cewa tun shekarar 2017 kusan duk mako kungiyar CNG na samun labarin yadda yan bindiga ke kashe ‘yan arewa mazaunan kudu ba’a daukan matakan da su ka dace a kan miyagun lamarin da ke kara tsananta musamman a baya-bayan nan.
Faifan bidiyo da ya nuna gawawwakin mutanen da lamarin ya rutsa da su dake ta yawo a kafaffen sada zumunta na ci gaba da jawo muhawara mai karfi inda wata ‘yar Najeriya mazauniyar kasar waje ke cewa dole a tabbatar da doka da oda, hukunta masu laifi ba tare da duba addini ko kabilarsu ba kafin a sami saukin lamarin.
Hajiya Zainab Ahmed wacce aka fi sani da Bint Hijaz a kafaffen sada zumunta, mai rajin kare hakkin bil’adama ta ce sun zura ido su ga iya gudun ruwan gwamnati kan ala'marin tana mai cewa idan gwamnati bata dauki mataki ba a game da wannan batu su zasu sake daura damara.
A nasa bangare, dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Yamatu Deba na jihar Gombe a tarayyar Najeriya, Alh. Yunusa Ahmad Abubakar, ya ce dole ne bangaren zartarwa su sake daura damara su yi hobbasa a fuskanci wannan kalubalen na tsaro.
Rahotannin dai sun yi nuni da cewa gwamnan Charles Soludo, na jihar Anambra da ‘yan sandan jihar sun yi Allah wadai da kashe mutanen sai dai wasu ‘yan Najeriya sun ce sun gaji da jin gwamnati na yin Allah wadai a maimakon daukan kwararran matakai.
A cewar wata majiya, matar mai ciki da ‘ya’yanta na kan hanyarsu ta komawa gida ne a kan acaba a lokacin da ‘yan bindiga suka yi musu kwanton bauna a yankin Orumba da ke jihar Anambra.
Ya zuwa lokacin hada wannan rahoton dai duk kokarin ji ta bakin gwamnatin tarayya dai ya ci tura.
Saurari cikakken rahoton Halima Abdul'ra'uf cikin sauti: