Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dole Ne A Hukunta Mutanen Dake Da Hannu A Kisan Sojoji A Jihar Delta -Majalisar Dattawa


Zauren majalisar dattawan Najeriya (Facebook/Nigerian Senate)
Zauren majalisar dattawan Najeriya (Facebook/Nigerian Senate)

Majalisar Dattawan Najeriya tayi alawadai da mummunan kisan gillar da aka yiwa dakarun aikin wanzar da zaman lafiya na "Operation Delta Safe" su 16 a kauyen Okuama dake karamar hukumar Ughelli ta Kudu a jihar Delta.

WASHINGTON DC - Da take martani game da kisan dakarun sojin dake kokarin wanzar da zaman lafiya tsakanin al'umomin Ukuoma da Okoluba, Majalisar a sanarwar data fitar a ranar Lahadi, tace wajibi ne wadanda keda hannu a lamarin su girbi abunda suka shuka.

Sanarwar dake dauke da sa hannun Shugaban Kwamitin Majalisar Akan Harkokin Soja, Abdul Aziz 'Yar-Adua tace har abada Najeriya ba zata manta da irin sadaukarwar da babban kwamandan da manyan hafsoshi 3 da kananan sojoji 12 suka bayar wajen wanzar da zaman lafiya ba".

"Ina mai yabawa matakin gaggawan da Babban Hafsan Tsaron Kasar nan ya dauka na bada umarnin gudanar da binciken gaggawa da nufin zakulo wadanda keda hannu a wannan mummunan lamari. Aniyar rundunar sojin Najeriya na tabbatar da zaman lafiya da tsaro shaida ce akan irin jajircewa da sadaukarwarta.

Sanarwar ta kara da cewar, Kwamitin Harkokin Sojin Majalisar Dattawa na tare da Rundunar Sojin Najeriya da shelkwatar tsaro wajen nemawa dakarun da aka hallaka hakkinsu. Baza muyi kasa a gwiwa ba wajen bada goyan bayanmu a harkar bincike da shari'a domin ganin wadanda suka kitsa wannan kisa sun girbi abinda suka shuka.

Haka zalika, a ranar Lahadi ne Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ba da umarnin hukunta duk wadanda ke da hanu a kashe dakarun rundunar sojojin Najeriyar.

A cikin wata sanarwa a ranar Lahadi, Tinubu ya ce “An baiwa hedikwatar tsaro da babban hafsan hafsoshin tsaro cikakken ikon gurfanar da duk wanda aka samu da hannu wajen aikata wannan aika-aika da aka yi wa al’ummar Najeriya. Ya kuma bayyana kisan a matsayin “jahilci.”

Ya kuma mika ta’aziyyarsa ga iyalan sojojin da aka kashe tare da bayyana aniyar gwamnatinsa na hukunta wadanda ke da hannu a kisan sojojin.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG