WASHINGTON, DC —
A yayin da sojojin Nijeriya ke cewa su na cigaba da fatattaka da kuma farautar 'yan kungiyar Jama'atu Ahlis Sunna Lid Daawati Wal Jihad, da ake wa lakabi da Boko Haram, su kuma mazauna jihohin da aka kakaba wa dokar ta bacin sun ce al'amarin na wajiga su; ga kuma rashin sadarwa ta wayar selula.
Wakilinmu na jihar Adamawa, Ibrahim Abdul'aziz, ya tattauna da wasu mazauna wadannan jihohin da su ka ce sanadiyyar kafa dokar ta bacin su na fama da talauci da rashin farinciki. Ga shi kuma babu damar su kira 'yan uwansu su dauke kewa su kuma yi zumunci.
Haka zalika, wasu 'yan Kungiyar Dattawan Arewa, Malam Abdulrazaq Yola da Barrister Solomon Dalong, sun yi Allah wadai da katse layukan sadarwan. Su ka ce ba haka ake yi ba a sauran wuraren da ake tashin hankali. Sun kuma yi zargin cewa ana gallaza wa jama'a ne kawai saboda tuni 'yan Boko Haram su ka ketara zuwa makwabtan kasashe da su ka ji za a far masu.