Dokar da ta fara aiki a Najeriya ranar daya ga watan daya na wannan shekarar ta 2017 rahotanni na nuni da cewa tuni kasashen Benin da Togo suka fara jin dokar a jikinsu.
Sakataren kungiyar dillalan motocin tokumbo na kasar Nijar Malam Aminu Umaru ya shaidawa Souley Mummuni Barma cewa dokar ta shafi kasashe da dama musamman Benin da Togo. Wadannan kasashen sunyi hasara sosai.
Kafin dokar ta fara aiki kasar Togo kadai na sayar da motoci fiye da dubu ishirin. Yanzu da kyar suke sayar da motoci dubu biyu ko uku a wata. A shekarun 2015 zuwa 2016 ta samu kudin shiga wajen dala miliyan talatin.Rashin zuwan 'yan Najeriya Cotonou sayen motoci ya sa tattalin arzikin kasar ya soma tabarbarewa.
Inji Malam Umar ko 'yan Nijar musamman wadanda suke arewacin kasar dokar zata zama masu matsala.
A Najeriya wasu masu sayar da motocin suna korafi akan rashin cikakken tsaro a birnin Legas. Alhaji Ibrahim Kato sabon shugaban kungiyar dillalan motocin a Najeriya reshen jihar Neja yace idan mutun ya sayi mota a Cotonou ba zai damu da rashin tsaro ba amma a Legas mutum na iya sayen mota a hannun dan damfara. Baicin hakan da mutum ya sayi mota Yarbawan Legas zasu ce dole su ne zasu tukata daga tashar jirgin ruwa zuwa a kalla Ibadan.
Alhaji Sani Ragada daya daga cikin shugabannin dillalan motocin a jihar Neja ya goyi bayan dokar. Yace idan sun je Lome ko Cotonou sayen mota sai sun bada cin hanci kafin su fitar da motar. Kamata yayi a taya gwamnatin Buhari farin ciki domin wani arziki ne yake son ya kawowa kasar.
Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari da karin bayani.