An nada gwarzon dan wasa Diego Maradona a matsayin kocin Gimnasia – wanda shine aikin horarwa na farko a kasarsu da ya fara tun daga shekarar 2010.
Tsohon dan wasan, mai shekaru 58, wanda shine kyaftin din Argentina wanda ya lashe Kofin Duniya a shekerara 1986, ya karbi ragamar kungiyar har zuwa karshen kakar wasa ta bana.
Gimnasia - wanda ake wa lakabi da El Lobo, wanda ke nufin 'The Wolf (wato dila)' - sune A kasan sashen Primera.
Maradona, wanda ya ci kyautar dan wasan kwallon kafa na FIFA a karni na 20 tare da Pele dan kasar Brazil, ya dauki kungiyar da ta samu maki daya daga wasanninta biyar da suka gabata.
Ya bar mukaminsa na baya a bangaren Dorados de Sinaloa ta Mexico a watan Yuni, saboda batun lafiyarsa, bayan da ya kasa jagorantar su zuwa gaba.
Wannan Sabon aikin na Maradona shine aikinsa na shida a gudanar da kulab; Ya kasance mai horar da 'yan wasan kasar na tsawon shekaru biyu daga shekarar 2008, inda ya jagorance su zuwa gasar cin Kofin Duniya na shekarara 2010 a Afirka ta Kudu.
Facebook Forum