Ana zantawar muryar Amurka da gwamna Dickson, yace muna cikin kasa daya Najeriya, inda kowamahaluki yake da ‘yancin yin walwala kamar yadda tsarin mulkin Najeriya ya tanada. A saboda haka yace baza a hana wani dan Najeriya, daga zuwa Kano ko sokoto ko Maiduguri ko Bayelsa ko kuma Enugu ba.
Ya kara da cewa a saboda haka suke son su samar da Najeriya, ta ‘yan uwantaka inda kow ane mahaluki yake ko takeda ‘yancin zama duk inda take so.
Yace a matsayinsa na gwamnan jihar Bayelsa kamar kuma yadda tsarin mulki ya tanada ya tabbata duk wani dan Najeriya da ke zaune a jihar alhaki ne da ya rataya a wuyansa ya tabbatar da yayi amfani da ikonsa domin kare kowa da kowa, yace abinida ya rika yi ke nan cikin shekaru biyar da suka shige kuma zai ci gaba da yin haka.
Gwamna Dickson, ya ci gaba da cewa ana nuna damuwa dangane da rikici tsakanin makiyaya da manoma da sauran al’umma. Hanyar data fi dacewa a magance wannan matsala itace a samarwa makiyaya ko daga ina suka fito wurin da zasu yi kiwo ba tare da tsangwama ba.
Yace alhaki ne daya rataya a wuyan shugabanin na tabbatar da cewa sun samar da irin wadannan wurare a saboda haka ne gwamnatinsa ta dauki wannan mataki. An samarwa makiyaya dukkan abubuwan da suka kamata a wannan yanki ko wuri da aka ware domin yin kiwo, to amma kuma yace makiyaya suna biyan haraji. Haka kuma yace binciken da aka gudanar ya nuna cewa a zahiri akwai makiyayan da suke yi wa wasu mutane kiwon shanun ma ba nasu bane.
Kuma bayan da gwamnan ya dauki wannan mataki sai aka yi zanga zanga suna zargin cewa yana so ya maida jihar ta zama ta Musulmi, yace babu kashin gaskiya a wannan batu babu wanda yake so ya maida jihar Bayelsa ta zama ta Musulmi don me ma za a yi haka.
Facebook Forum