Dan wasan tsakiya na kungiyar kwallon kafa ta Manchester City dan kasar Spain David Silva, ya ce lokaci yayi kusa da zai bar kulob din, bayan ya shafe shekara 10 yana taka leda a kungiyar.
David mai shekaru 33 da haihuwa, yace a karshen kakar wasan shekarar 2019/20, zai bar kulob din, kafin nan dan wasan ya samu nasarar lashe kofin Firimiya lig sau hudu, kofin kalu bale na (FA) biyu da kuma kofin Lig hudu tun bayan da ya koma kungiyar a shekarar 2010, ya buga wasannin har guda 395.
A kakar wasan Firimiyar lig da ta gabata ya buga wasanni 33, ya zura kwallaye har shida ya taimaka wa kulob din sake lashe kofin a karo na biyu a jere, kar kashin jagorancin mai horas da ita Pep Guardiola.
Silva ya kara da cewa wannan ita ce shekararsa ta karshe da zai fafata a kulob din, domin shekara goma kenan cif-cif yana kungiyar Man City, kuma
klob din ya ishe shi.
Manchester City sun bukaci ya sake sa hannu kan yarjejeniyar kwantirakin shekaru biyu, amma sai ya yanke shawarar zai kara daya kacal.
Facebook Forum