Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Daruruwan 'Yan Libiya Sun Yi Zanga Zangar Kin Gwamnati


Dadadden Shugaban Libiya, Moammar Gadhafi da ke fuskantar zanga-zangar nemar ya sauka.
Dadadden Shugaban Libiya, Moammar Gadhafi da ke fuskantar zanga-zangar nemar ya sauka.

Daruruwan ‘yan Libiya sun yi zanga-zangar kin gwamnati a birni na biyu a girma a kasar, wato Benghazi, inda su ka yi ta rairai kalaman nuna bijirewa ga shugabannin Libiya, su na ta fafatawa da ‘yan sanda.

Daruruwan ‘yan Libiya sun yi zanga-zangar kin gwamnati a birni na biyu a girma a kasar, wato Benghazi, inda su ka yi ta rairai kalaman nuna bijirewa ga shugabannin Libiya, su na ta fafatawa da ‘yan sanda.

Shaidun gani da ido da kuma kafafen yada labarai masu zaman kansu sun ce masu zanga-zangar sun fara taruwa ne tun daga yammacin jiya Talata zuwa safiyar yau Laraba a harabar wani ginin jami’an tsaro a birnin Benghazi, inda da farko su ka bukaci sai dai a sako wani lauya wanda fitaccen mai sukar gwamnati ne.

Kafafen yada labaran Libiya sun ce an sako lauyan, to amman sai kuma masu zanga-zangar su ka cigaba da karuwa su ka kuma shiga raira kalaman nuna kiyayya ga gwamnati. Rahotannin sun ce wasu daga cikin masu zanga-zangar sun yi ta jejjefa ‘yan sandan da duwatsu bayan ‘yan sandan sun yi kokarin korarsu. Wata jaridar Libiya t ace mutane 14 sun sami raunuka.

Kafafen yada labarai mallakin gwamnatin Libiya sun ki yada labarin zanga-zangar, sai kawai daga bisani suka bayar da labarin cewa wasu magoya bayan gwamnati sun yi zanga-zanga a birnin Benghazi da babban birnin kasar, Tripoli da sauran birane.

‘Yan gwagwarmayar adawa a Libiya sun yi ta amfani da kafafen sadarwa ta internet wajen kiran taron kaddamar da zanga-zangar kin gwamnati a gobe Alhamis, bayan sun sami kwarin gwiwa daga zanga-zangar da su ka yi sanadin hambarar da shugabannin masu kama karya a Misra da Tunisia cikin ‘yan makonnin nan.

Shugaban Libiya Moammar Gadhafi na bisa gadon mulkin tun cikin shekara ta 1969, bayan day a shugabanci juyin mulkin da aka yi wa masarautar kasar da ke samin goyon bayan yammacin duniya.

XS
SM
MD
LG