Rohotannin da ke fitowa daga Jihar Yobe na nuna cewar gungun mayakan Boko Haram ne suka zo cikin kakin sojin a motoci masu fentin sojoji dauke da muggan makamai zuwa sansanin sojin Najeriya da ke a wani kauyen Jilli, a Jihar Yobe da ke kan iyaka da Jihar Borno, tsakanin yankin Tafkin Chadi, inda suka bude wuta sosai akan mayakan Najeriya har suka ci karfinsu.
Garin Geidam da ya kasance hedikwatan masarautar Gazargamu, na kan iyaka da Jamhuriyar Nijar kuma a nan ne tungar mayakan Boko Haram bangaren Abu Mustapha Al-Barnawi.
Bayan wannan arrangamar, rohotanni na nuna cewar, kimanin sojojin Najeriya 600 ne suka bace ba labarinsu, yayin da kimanin 100 sun shiga garin Geidam, wasu daga cikinsu, ba tare da makamansu ba.
A jihar Borno da ke makwabtaka da jihar Yobe, rohotannin da ke fitowa daga can, na nuna cewa mayakan Boko Haram sun kai wani wawan hari akan ayarin sojin Najeriya a kauyen Bulagalayye da ke tsakanin Bama da Dikwa inda nan ma soji masu yawan gaske suka rasa rayukansu da kuma 'yan sa kai.
A yayin da hedikwatar sojin Najeriya ta yi shiru akan harin na Jihar Yobe, kakakinta Birgediya Janar Texas Chukwu, ya fitar da sanarwa kan harin na Jihar Borno inda ya ce soji daya ne ya rasa ransa, guda kuma ya jikkata. Ya kuma bayyana cewa munin harin bai kai yadda ake ta yayatashi ba.
Wasu masu tsokaci kan lamuran tsaro, na ganin wannan koma bayan da ake samu na baya-bayannan a yaki da ta'addanci a Najeriya, gazawa ne na manyan hafsoshin tsaron kasar.
"Shugabannin tsaron sun gaza," inji mai sharhi kan sha'anin tsaron Najeriya, Mallam Shu'aibu Mungadi.
"A can baya mun ji suna kukan cewa basu da kayan fada, da kudi, da sauransu, amma yanzu ba mu ji suna kukan ba su da isasshen kayan fada ba, ko gwamnatin tarayya ta daina ba su kudi, don haka kenan gwamnati na bayar da kudi, 'yan majalisa suna sa hannu domin bukata idan ta taso."
Masanin tsaron ya kuma dorawa Shugaba Buhari laifi akan wannan lamarin.
"Gazawar da Shugaban kasa yayi a cikin wannan sha'anin tsaron Najeriya shine, kunnen uwar shegun da yayi ga kiran 'yan Najeriya na a yi garambawul ga sha'anin tsaro, domin duk ya sabunta masu wa'adin aikinsu. Babu dalili ana ci baya ga aiki kuma kana sabuntawa."
Facebook Forum