Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dansanda Ne Ya Harbe 'Yansanda A Kenya Ba Dan Al-Shabab Ba


'Yansandan kuntunbala na Kenya sun kewaye ofishinsu dake Kapenguria inda suke kashe maharbin
'Yansandan kuntunbala na Kenya sun kewaye ofishinsu dake Kapenguria inda suke kashe maharbin

Wanda ya harbe 'yansanda shida har lahira a Kenya, a harabar ofishinsu, dake yammacin Kenyan yau Alhamis, jami'in 'yansanda ne kamar yadda wani ganau ya shaida

Rahotanni da suka fara fitowa ta kafofin labaran kasar Kenya da na kasa da kasa sun ce maharbin wani da kungiyar al-Shabab ne da 'yansandan ke tsare dashi wanda yake samar ma kungiyar kurata.

Amma wasu jami'an 'yansandan su biyu da basu so a bayyana sunayensu ba sun ce dansanda ne ya harbe abokan aikinsa har guda shida ba dan kungiyar al-Shabab ba.

Sunan dansandan da yayi harbin Maslah. "Da zuwansa aiki yau da misalin karfe 4 na safe, sai ya dauki bindigarsa ya harbe jami'an 'yansanda guda biyar, bayan dan lokaci sai ya sake harbe mutum daya", inji wani dansandan yayinda da ya yi magana da Muryar Amurka sashen Somalia..

Wani dansandan da yaki ya bada sunasa yace yana cikin wadanda suka fara amsa kira domin kai doki a ginin. Yace maharbin wani mutum ne mai cike da bakin ciki"

Yace "na san mutumin. Sunashi Maslah. Dan asalin Somali ne ya zama dan Kenya kafin ya shiga aikin 'yansanda. Ya mika wasikar yin murabus daga aikin yana jira wata da watanni ba'a bashi amsa ba. Ina jin abun da ya sa ya hasala ke nan har ya harbe mutane", inji shi.

'Yansandan da suka kawo taimakon ceto wurin sun harbe maharin a ofishinsu dake Kapenguria.

Tun farko babban sifeton yansandan Joseph Boinnet ya fada a jawabin da ya yi cewa 'yansandan kuntunbala su ne suka kewaye ginin saboda kawo karshen turjiyar na maharbin.

XS
SM
MD
LG