Dan wasannan me tsaron gida na kungiyar kwallon kafar Southampton, Toby Alderweireld, yace yana so ya zauna a kulob in Southampton, da dai ya koma kungiyar Atletico Madrid, da zarar kwantirakin shi ta kare a karshen wannan kakar wasannin.
Shi dai dan wasan Alderweireld, ya na cikin yarjejeniyar me tsawo a wannan kakar da kungiyar Atletico Madrid, wadda ta lashe wasan zakaru na La Liga. Ita kuwa kungiyar kasa-da-kasa ta Belgium, tazamo mamba a tawagar klob in Southamptom, tun bayan komawar su filin wasan St Mary, a watana satumba.
Shi dai dan wasan me shekaru 26, ya buga wasanni har so 16 a lokacin zaman shi da shugaban klub in Mr. Ronald Koeman, wannan dai kan iya zama wani abun rashin jituwa a tsakaninsu a kakar wasannin me zuwa.
Dan wasan dai ya bayyanar da cewar zai so ya zauna a kungiyar ya buga mata wasa har ya wuce kakar wasannin na shekar 2015, duk dai da cewar matakin karshe na hannun shuwagabannin kungiyar Atletico Madrid.
-
Yusuf Harande
Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.