Dan wasan Barcelona Lionel Messi, ya zura kwallo ta 108 a gasar cin kofin zakarun Turai. Messi ya samu wannan nasara ne bayan da ya ci kwallaye biyu a wasan da Barcelona ta doke Lyon da ci 5-1, ranar Laraba a Camp Nou.
Sai dai har yanzu bai kai Cristiano Ronaldo na kungiyar Juventus ba, wanda ya zurara kwallaye 124 jumulla a gasar ta zakarun nahiyar turai.
A karon farko kenan da Barcelona za ta wakilci Spain ita kadai a zagaye na gaba wato (Quarter Final), cikin gasar zakarun Turai tare da kungiyoyi da suka hada da Juventus da Ajax, da FC Porto.
Kungiyoyin kwallon kafa hudu daga kasar Ingila, da suka hada da Manchester United, Manchester City, da Liverpool, da Tottenham, su kuma zasu wakilci kasar cikin gasar.
Rabon da ace kungiya daya ta rage a gasar zakarun turai daga Spain a irin wannan matakin tun bayan shekarar 2010.
Facebook Forum