Dan wasan tsakiya na kungiyar kwallon kafar Liverpool, mai suna Fabinho zai tafi dogon jinya har zuwa sabuwar shekarar ta 2020.
Dan wasan dan kasar Brazil mai shekaru 26 da haihuwa, ya samu rauni a idon sawunsa (ankle ligament damage) cikin mintuna 19 da fara wasan da suka fafata da Napoli, cikin gasar rukuni na cin kofin zakarun turai (Uefa Champions League) a bana, inda suka tashi 1-1 a Ingila ranar Laraba da ta gabata.
Kocin kungiyar Jurgen Klopp, yace rashin dan wasa kamar Fabinho babban abun bakin ciki ne, da kuma rashi ga kungiyar da magoya bayanta ne.
Duk da dai bamu da tabbacin cewar zai kai tsawon lokacin da ake hasashe, amman dai dan wasan baya daya daga cikin tawagar da zasu fafata wa kulob din a karawar su da Liverpool a cikin wasannin kirsimetin bana inji kocin.
Sai yace ya zamo dole su nemi wanda zai maye gurbin sa kafin ya murmure da rashin lafiyar.
Dan wasan ya fara wasanni 12 cikin sha uku da Liverpool ta buga a gasar firimiyar bana.
Kana kungiyar na mataki na daya a teburin Lig din da tazarar maki 8 tsakaninta da mai biye da ita Leicester City.
Facebook Forum