Kayan da kumbon SpaceX ya yi jigilarsu sun isa tashar kumbon sararin sama ta kasa-da-kasa bayan kaddamar da kumbon a karshen makon da ya gabata, a jiya Litinin kayayyakin suka isa tare da rakiyar wasu 'yan kasar Kanada biyu.
Kumbon mai lakabin Dragon ya kai kayan mai nauyin kilo 2,500 da suka hada da na’urori da kayan gyara da dai sauran su.
Dan sama jannatin na kasar Canada mai suna, David Saint-Jacques, ya yi amafani da wani babban hannu na na’urar Robot a sararin samaniyar, wanda aka kera a Canada don ya dauki hoton kumbon na Dragon da aka kiyasta ya kai nisan kilomita dari hudu (400 km), a sama da arewacin tekun Atlantica.
Saint –Jacques, ya zama dan kasar Canada da ya yi amfani da kumbon sama jannati ya kai ziyara, a cewar hukumar kula da sararin samaniyar kasar Canada.
Facebook Forum