Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Coronavirus: Ku Taya Dana Da Addu'a - Atiku


Atiku Abubakar
Atiku Abubakar

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar ya bayyana cewa dansa ya kamu da cutar Coronavirus wacce ta addabi duniya gaba daya.

Ya bayyana hakan ne kan wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter da daren jiya.

A sakon ya ce an kai dan nasa zuwa Asibitin Kwararru da ke Gwagwalada domin a kula da shi.

Ya kuma kara da cewa yana rokon al’ummar Najeriya da su yi wa dan nasa addu’a.

A cewar hukumar dakile yaduwar cututuka a Najeriya NCDC, ya zuwa yanzu dai mutum 30 ne aka samu cewa suna dauke da cutar a Najeriya.

Mutum 22 a jihar Legas, mutum 4 a Abuja, 1 a Ekiti da 2 a Ogun da kuma 1 a Oyo.

Daga cikin mutane 30 din, mutum 2 sun warke daga cutar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG