Har yanzu ana ci gaba da dambarwa a game da halalci ko rashin halalcin zaben da aka yi ma Bukola Saraki a matsayin shugaban majalisar dattijan Najeriya, a yayin da wani tsohon gwamna kuma sanata yake bayyana mamakin ganin yadda aka dauki mukamin shugaban masu rinjaye aka ba David Mark.
Sanata Barnabas Gemade, dan jam'iyyar APC daga Jihar Binuwai, kuma daya daga cikin jigogin masu adawa da Bukola Saraki, yace yawan 'yan majalisar da suka taru suka zabi Saraki, bai kai adadin da doka ta bukata domin jefa kuri'a ba.
Sanata Dino Melaye, ya kare zaben Saraki da cewa ana bukatar sanatoci guda 38 ne kawai, watau sulusin sanatocin, domin iya zama da zartas da wani kuduri.
Wani masanin tsarin mulki, barrister Yakubu Saleh Bawa, yace wannan duk zai danganci irin fassarar da kotu zata yi ma tanadin tsarin mulki dangane da adadin sanatocin da ake bukata don zartas da kuduri, shin sai an rantsar da majalisa ta fara aiki ne wannan tanadin yake aiki ko kuma tun ma kafin a rantsar da su?