Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dalilin Da Ya Sa Na Ce Lokacin Sauyawa Najeriya Fasali Ya Yi - Babangida


Tsohon shugaban Mulkin Soja a Najeriya Janar Ibrahim Babangida
Tsohon shugaban Mulkin Soja a Najeriya Janar Ibrahim Babangida

A hirar da ya yi da Muryar Amurka tsohon shugaban Najeriya Janar Ibrahim Babangida ya ce lokaci ya yi da za'a ragewa gwamnatin tarayya iko a ba jihohi saboda ko a lokacinsa sun kafa kwamitin da zai duba sake tsarin mulkin kasar.

Tsohon shugaban Najeriya Janar Ibrahim Badamasi Babangida ko IBB, ya yi wa Muryar Amurka karin haske akan sakonsa na barka sallah da ya yi wa kasar.

A cikin sakon ya ce yanzu lokaci ya yi da ya kamata a ce an yi kwaskwarima akan fasalin Najeriya ta yadda za'a rage nauyin iko ga gwamnatin tarayya a maida wa jihohi.

Babangida ya bayyana cewa "akwai surutai da yawa na tashin hankali da hayaniya kuma ba su dace ba. Kasa har yanzu tana kokari ta samu kanta cikin sauran kasashen duniya shi ya sa na ba da shawara a yi haka."

Akan cewa abun da yake son a yi yanzu ya na da wuya sai ya ce "ba sabon abu ba ne . Mun dade muna magana. Har kwamiti mun sa da zai duba wannan. Yau ina yi maka batun shekaru 24 da suka wuce, domin na bar ofis yau shekara 24. Kafin lokacin mun kafa kwamiti su duba yadda za'a rarrage wasu abubuwa da Federal Government (gwamnatin tarayya) ta ke rike da shi a maida wa states (jihohi)."

Da yake tsokaci akan masu bukatar kasar ta dare biyu a kafa kasar Biafra sai tsohon shugaban ya ce " Najeriya kasa daya ce ga yadda muka sani da kuma yadda constitution (tsarin mulki) din mu ya bayar saboda haka maganar a raba ba ta taso ba. Mun je yaki saboda irin wadannan hayaniyar ce...A yi zagi duk basu da amfani. Amma idan aka iya zama da hankalinmu a tattauna a san yadda za'a daidaita"

Shi ma tsohon gwamnan jihar Kano Kanar Sani Bello mai ritaya ya ce raba Najeriya ba shi ne alheri ba a yanzu.

Ya ce girman kasa ma shi kanshi ya na ba kasa daraja. ya na mai jaddada cewa ba a cika damawa da kananan kasashe ba.

Amma "babbar kasa kamar Najeriya dole ne a yi magana da mu" Ya roki mutanen Najeriya da a zauna lafiya.

Ga karin bayani a rahoton Mustapha Nasiru Batsari.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00

Facebook Forum

TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Kamala Harris Ta Amince Da Shan Kaye A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Sakamakon Zaben 2024 A Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG