Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dalilin Da Ya Sa Jiga-Jigan Gwamnati Ke Kamuwa Da Corona


Ministan harkokin waje a Najeriya, Geoffrey Onyeama
Ministan harkokin waje a Najeriya, Geoffrey Onyeama

‘Yan Najeriya na ci gaba da tafka muhawara kan yadda manyan jiga-jigan gwamnatin kasar wadanda ke kan gaba wajen fadakarwa tare da yin yaki da annobar Coronavirus ke ci gaba da kamuwa da cutar.

Wannan lamari ya janyo fargaba a tsakanin sauran ‘yan kasar musamman marasa karfi wadanda ke aiki a karkashin ma’aikatan gwamnati kamar masu gadi, 'yan aikin gida, masinjoji da dai sauransu.

Tun farkon bullar cutar a Najeriya ya zuwa wannan lokaci, wasu ‘yan kasar ke ta bayyana mabambantan ra’ayi a kan yiyuwar yaduwarta a tsakanin marasa karfi musamman wadanda ba su da damar ketarawa kasashen duniya.

Akwai rahotanni da dama da ke tuna chew wasu ma ba su yarda cutar ta shiga kasar ba har sai da marigayi Malam Abba Kyari, tsohon shugaban ma’aikatan fadar shugaban Najeriya ya kamu da cutar, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwarsa.

Wanda ya kamu da cutar a baya-bayan nan cikin jiga-jigan gwamnatin kasar da ya ja hankalin jama'a shi ne Ministan harkokin waje, Geoffrey Onyema, wanda wasu masu sharhi suka ce yanayin cudanyarsa da mutane ya sanya shi cikin hatsarin kamuwa da cutar.

Wasu manya na daban da suka kamu da cutar sun hada da Nasir El-Rufai, gwamnan jihar Kaduna kuma gwamna na farko a Najeriya na farko da ya kamu da cutar.

Sai kuma gwamna Bala Muhammad na Bauchi da gwamna Seyi Makinde na Oyo da Rotimi Akeredolu na Ondo da dai sauransu.

Gwamna Nasir El-Rufai
Gwamna Nasir El-Rufai

Dr. Sani Hammad daga asibitin koyarwa na Barau Dikko a jihar Kaduna ya yi wa Muryar Amurka karin bayani inda ya ce ba a Najeriya kawai lamarin ya kasance hakan ba.

"Mun lura da yadda manyan jiga-jigan gwamnati ke kamuwa, amma ya kamata mu sani cewa a sauran kasashen duniya ma haka lamarin yake."

"Dole ne su yi cudanya da mutane domin su yi mulki yadda ya kamata, sai kuma yawancinsu shekarunsu ya hau saboda haka sun fi mutane da yawa hadarin mutuwa."

Wani batu na daban da ya sa ake yawan ganin cewa jiga-jigan gwamnati cutar ta fi kamawa shi ne yadda ake bayyana kusan komai na rayuwarsu kai tsaye a matsayinsu na fitattu a cikin al’uma.

Ya zuwa yanzu dai mutum 37,801 ne suka kamu da wannan cutar a Najeriya, yayin da mutum 805 suka rasa rayukansu.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG