Jamia’ar Damagaran a Jamhuriyar Nijar na fuskantar matsalar ci gaba da tafiyar da harkokin koyarwa a cikin ta.
Wannan ne yasa ministan Ilmi na kasar Yahuza Salisu Madobi yin tattaki zuwa jamia’ar domin ganawa da hukumominta da kuma na dalibai.
Sakataren kungiyar Daliban Mamman Malam Bukar yace fatar su shine a samu maslaha da zata kawo karshen matsalolin da suke addabar jamia’ar.
Malam Bukar yace kungiyar su ce ta gayyato ministan ilmi domin ya gane wa idanun sa abinda ke faruwa da niyyar ayi gyara akai.
Yace yana fata wannan tattaunawar ta zarta na zaman shan shayi da aka saba yi a lokuttan baya, domin jami’aar ta kwashe shekaru tana fama da matsaloli iri daba-daban.
Ga Tamar Abari da karin bayani 2’53:
Facebook Forum