WASHINGTON, DC —
Shahararren masani kan harkokin yau da kullum da siyasa da zamantakewar dan adam Dakta Dukawa yayi furuci kan abubuwan da ya hango zasu kawo cikas a taron kasa.
Daga cikin maganganun da aka sha yi shi ne fargabar da ake da ita cewa taron ba zai iya warware matsalolin Najeriya ba. A ganinsa kuma kamar biri yayi kama da mutum idan aka yi la'akari da abun da ya faru cikin kwana uku da soma taron.
Dakta Dukawa yace yadda wakilan taron suka kama ludayin taron abubuwa biyu suna da ban tsoro. Matsala ta daya ita ce kasa yaddan wakilan kan kuduri na goma sha daya inda aka ce idan an zo kada kuri'ar raba gaddama a tsayar da kuri'un da za'a ce idan an samu za'a yadda da kudirin. Idan kuri'u basu kai yadda aka tsayar ba sai a ki yadda da kudurin. To kasa yadda da wannan shirin zai kawo matsala.
Abu mai muni kuma shi ne yadda wakilan suka tsayar da karbar kudiri kan kudu da arewa. Wato akwai abunda wakilan kudu zasu yadda da shi akwai kuma wanda wakilan arewa zasu yadda da shi. Tsayar da kuduri kan kudu ko arewa ba zai haifarwa kasar wani da mai ido ba. Ma'ana sun sauka daga doran cewa wace kaida ce zata yiwa kowa adalci saboda haka a dauketa. Amma sun kauce ma wannan sun koma kan kudu da nata arewa kuma da nata. Idan an tsaya kan wace kaida ce kudu ta fi so ko kuma wace kaida ce arewa ta fi so, to ba shakka ba za'a fitar da kasar daga komi ba. Kamata yayi wakilan su jefa kuri'a kan kaidar da zata fi taimakawa Najeriya gaba daya ta kuma kawo cigaban kowa da kowa cikin lumana da adalci da hadin kai.
Amma idan aka cigaba da yin abubuwa kan kudu da arewa kudu da arewa kasar ba zata anfana ba.
Ga karin bayani.