Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dage Zabe: MDD, ECOWAS, Sun Rarrashi ‘Yan Najeriya


Shugabannin ECOWAS a taronsu a Abuja, Disamba 16, 2015.
Shugabannin ECOWAS a taronsu a Abuja, Disamba 16, 2015.

Shugabannin wakilan da ke sa ido kan zaben Najeriya na kasa da kasa, tare da hadin gwiwar Majalisar Dinkin Duniya, sun rarrashi ‘yan Najeriya kan dage babban zaben kasar da hukumar zabe ta INEC ta yi, tare da yin kira da su marawa hukumar ta INEC baya.

Shugabannin sun yi wannan kiran ne a jiya Asabar, a wata sanarwa ta hadin gwiwa da suka fita, bayan da hukumar zaben ta Najeriya ta ayyana dage babban zaben kasar daga jiya 16 ga watan Fabrairu zuwa 23.

“Duk da cewa wannan shawara da hukumar ta INEC ta yanke ba ta yi wa mutane da yawa dadi ba, muna kira ga ‘yan Najeriya da kada su hasala, su kuma ci gaba da nuna goyon baya ga shirye-shiryen zaben, yayin da hukumar ta INEC ke kokarin ganin ta aiwatar da sabon jadawalin da ta fitar.” Sanarwar wacce ke dauke da sa hannun shugabannin ta bayyana.

Sai dai shugabannin, sun yi kira ga hukumar zaben da ta yi amfani da wannan lokacin da ta diba, wajen ganin ta gudanar da zaben kamar yadda ta tsara.

Shugabannin sun kuma yi kira ga INEC da ta rika fitar da bayanai ga jama’a kan halin da ake ciki game da shirye-shiryen zaben a cikin kwanaki masu zuwa domin bai wa jama’a karfin gwiwar amincewa da shirye-shiryen.

“Yayin da muke ci gaba da lura da shirye-shiryen a duk faɗin ƙasar, muna mika goyon bayan mu ga al’ummar Najeriya domin ganin an gudanar da sahihin zabe cikin lumana da kwanciyar hankali.”

Shugabannin da suka rattaba hannu a wannan sanarwa ta hadin gwiwa, sun hada da wakiliyar tawagar kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka kuma tsohuwar shugabar kasar Liberia,Ellen Johnson Sirleaf, da wakiliyar kungiyar tarayyar turai Maria Arena, da wakilin babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, a yammacin Afirka da yankin Sahel, Mohammad Ibn Chambas da dai sauransu.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG