Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Da Kaina Zan Fita Gadin Hanya Ranar Sallah – El Rufa’i


Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai
Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai

A wani mataki na dakile yaduwar cutar COVID-19, Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru El Rufa’i ya ce shi da kansa zai fita sintirin gadin kan iyakar jihar da Kano domin hana mutane shiga garin.

El-Rufai ya bayyana wannan mataki ne yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai a wani jawabi na kai-tsaye da ya yi ta kafafen yada labarai wanda ya yi ga al'umar Kaduna.

“Ranar Sallah ni ne mai gadin hanyar Kano, mataimakiyar gwamna mai gadin hanyar Katsina da Zamfara, Sakataren gwamnati shi ne mai gadin hanyar Abuja, mu ga wanda zai shigo mana gari.” Gwamnan ya ce.

Tun dai gabanin hakan, Jihar ta Kaduna ta garkame hanyoyin shiga yankinta domin dakile yaduwar cutar ta COVID-19.

Jihohi musamman a arewacin Najeriya na ta daukan matakan takaita cudanya a tsakanin al’uma yayin da musulmi a sassan duniya ke shirin gudanar da bukukuwan sallah.

Bayyana wannan mataki har ila yau na zuwa ne yayin da ake ta ka-ce-na-ce dangane da matakin hana sallar Idi da hukumomin jihar suka dauka gudun kada a yada cutar ta coronavirus.

A cewar El Rufai addinin musulunci ya yarda cewa tafarnuwa ma tana hana jam'in sallah ballantana cutar corona da ta addabi duniya.

“Mutane ba su son gaskiya, ya ya za a daura muhimmancin zuwa jam’i kan ran mutum?"

A cewar gwamnan, “sun dauka mu jahilai ne?"

Yawo da kuma karbar baki na cikin dalilan da suka kawo cutar corona cikin jihar ta Kaduna in ji gwamna El-rufai, saboda haka ya ce a yi zumunci a waya.

Yanzu dai dokar ta zaman gida ta haura wata biyu a jihar Kaduna, abin da ya sa wasu ke tambayar ko yaushe ne za a bude jihar.

Mataimakiyar gwamnan jihar Kaduna, Dr. Hadiza Sabuwa Balarabe ta ce, “sai mun tabbatar cewa an samu sauki tukunna, sannan za mu fara tunanin tsara yadda za a bude jihar a hankali.”

Ya zuwa yanzu mutum 152 ne cutar ta kama a jihar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG