Washington, DC - Sarkin garin Kanje Aliyu Hashim, ya ce masarautar ta kafu ne tun a lokacin Usman Danfodiyo fiye da shekaru 200 da suka wuce.
Yakubun Bauchi, na daga cikin wadandan suka kafa garin, amma Munka’il Guraguri shi ne ya fara sarauta karon farko a garin.
Garin Kanje ya kunshi kabilun Jukunawa, Kanuri, Katsinawa da sauransu. Kuma ana yi masa kira da “Kanji Kangiya Kan Kura.”
Garin ya yi suna ta fannin jihadi a lokacin Usman Danfodio, bayan haka ya kuma shahara wajen noma da farauta.
Saurari cikakken shirin cikin sauti.