Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Da Dan Gari: Tarihin Garin Aloshi, Jihar Nasarawa


Shirin Da Dan Gari na wannan makon ya kai ziyara garin Aloshi a karamar hukumar Keana da ke jihar Nasarawa, a karkashin jagorancin gidan rediyo da talabijin din jihar Nasarawa.

Sarkin garin Aloshi Alhaji Muhammad Agye Usman, wanda shi ne basaraken garin na 18, ya bada dan takaitaccen tarihin garin inda ya bayyana cewa garin ya shahara a harkar noma da kiwo.

Alhaji Agye ya kuma ce wasu daga cikin matsalolin da garin ke fuskanta sun hada da rashin ruwa, ingantattaun hanyoyi da makarantu, ya kuma yi kira ga gwamnati da ta taimaka musu.

Saurari cikakken shirin wanda Sadiq Abbas ya gabatar.

Da Dan Gari: Tarihin Garin Aloshi, Jihar Nasarawa
please wait

No media source currently available

0:00 0:11:30 0:00


XS
SM
MD
LG