Daga dukkan alamu za'a kai ruwa rana tsakanin shugaban kasar Gambia, mai barin gado Yahaya Jamme, da wakilan kasashen Afirka, ta yamma, ta aka sa su gana dashi domin a warware takaddamar dake kasar dangane da furicinsa na kin son mika mulki ga shugaba mai jiran gado.
Yahaya Jamme, dai a ‘yan kwanakin nan ya ce ba zai mika mulki ga sabuwar Gwamnatin da aka zaba ba saboda magudin da yake zargin cewa an tafka, yana mai tabbatar da cewa tuni ya kai kara ga kotun kolin kasar na kalubalantar zaben.
Ganin cewa shuwagabanin kasashen Afirka, ta yamma da majalisar dinkin duniya,suna kurarin cewa sai an tabbatar da wannan zabe da aka yi, kakakin shugaba Muhammadu Buhari, Malam Garba Shehu, ya ce ana shirye shiryen fara sauraran wa’anda suke jayayya da juna ta inda za’a ji abubuwan da shugaba mai jiran gado menene manufofinsa game da shugaba mai barin karagar mulki.
Bababr manufa shine duk abinda za’a yi ayi maganin fitina kada ta tasu a Gambia, shine za’a yi domin idan fitina ta tashi ba’a san inda zata tsaya ba.