Cutar Kolera ta abkawa Nigeria da Kamaru kuma tayi barna a cikinsu don kuwa ta hallaka mutane 200 a Kamaru, 40 a Nigeria. A jiya ne wani kusar na gwamnatin Nigeria yake fadar cewa akwai akalla mutane 1,200 da suka kamu da cutar a jihar Borno kadai dake Nigeria inda daga can ne ma abin ya samo asali. A arewancin Kamaru ma rahottani sun ce mutane kusan 2,300 suka kamu da cutar daga lokacinda ta fara bulla a farkon watan Mayu.
Cutar kolera ta hallaka mutane da dama, ta kuma kama da yawa a kasashen Nigeria da Kamaru.