Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Cutar Ebola Ta Yadu Zuwa Birnin Mbandaka


Bayanai daga Jamhuriyar Damokaradiyar Kwango na nuni da cewa cutar Ebola da ta barke a kasar da tayi sanadain asarar rayuka ta fara bazuwa zuwa wadansu garuruwa.

Hukumar Kiyon lafiya ta duniya, watau WHO, ta ce barkewar cutar Ebola a Jamhuriyar Damokaradiar Kwango ya yadu zuwa wani birnin kasar, abinda ke hadasa fargabar wanzuwar cutar mai hallaka mutane.

An tabbatar da bullar cutar a cikin daya daga yankunan da aka kebe na musamman dake garin Mbandaka mai mutane fiye da miliyan daya , wanda kuma yake a arewa maso yammacin lardin Equateur. Mbandaka na da tazarar kilomita 150 daga yankin karkarar Bikoro, inda anan ne bullar cutar ta samo asali a farkon wannan watan.

Shugaban hukumar ta WHO Dr. Tedros Adhanom Ghybreysues ya ce wannan al’amarin abin damuwa ne.

A yanzu dai Hukumar ta ce zata aika kwararu 30 zuwa birnin na Mbandaka don su nazarci lamarin.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG