A karon farko cikin wannan shekarar an samu karuwar wadanda suka kamu da cutar ebola a kasashen yammacin Afirka uku inda har yanzu ake fama da cutar.
Hukumar kiwon lafiya ta duniya ko WHO a takaice tace an samu mutane 124 da suka kamu da cutar a karshen makon jiya.
Kasar Saliyo ce take kan gaba inda mutane 80 suka kamu. Sai kasar Guinea inda aka samu 39. A Liberiya kuwa an samu mutane biyar.
A wani sabon rahoto da hukumar kiwon lafiya din ta fitar jiya Laraba tace akwai bukatar a gaggauta a shawo kan sabuwar barkewar kafin damina ta kankama lokacin da shiga kauyuka zai yi wuya.
Tun lokacin da annobar ta barke mutane kusan 22,500 suka kamu da cutar a kasashe uku kuma adadin wadanda suka mutu ya dara 9,000.
Cutar tayi kamar ta tsaya domin an samu makonni da dama babu sabbin kamu.
Dama kwararru a kiwon lafiya sun yiwa yankin yammacin Afirka din kashedi cewa kada su saki jiki domin cutar ka iya dawowa.
Hukumar kiwon lafiya ta duniya tace jana’izar da aka yi a yankin Lola a kasar Guinea watan jiya ba bisa bin ka’idodin da ta tsara ba yayi sababin da mutane 11 suka kamu da cutar.
Wajibi ne a bi ka’idodin binne gawa domin mutane na iya kamuwa da cutar idan itace tayi sanadiyar mutuwar.
Ranar Litinin din nan aka fara gwajin allurar rigakafin cutar a kasar Liberia.