Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Cutar Dabbobi Ta Yi Sanadiyar Mutuwar Mutane 22 A Nijar


Halaru Shaibu na ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar Nijar
Halaru Shaibu na ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar Nijar

Sakamakon binciken jinin wadanda annobar ta cutar dabbobi ta rutsa dasu ya nuna cewa wadanda suka mutu, cutar ce sanadiyar mutuwarsu.

An gano kwayar dake cikin dabbobin da suka mutu a cikin mutanen da suka rasu a yankin Tawa a Jamhuriyar Nijar.

Daga cikin mutane hamsin da aka tabbatar sun kamu da cutar a sakamakon annobar, kimanin 22 suka mutu kamar yadda Halaru Shaibu, babban jami'in ma'akatar kiwon lafiya a bangaren maganin rigakafin cututtuka ta Nijar ya sanar.

Yace lokacin da cutar ta bullo sun gayawa mutane magungunan da zasu yi anfani dasu domin kaucewa kamuwa da kwayar cutar. Cikin mutane hamsin da suka kamu su hamsin kafin a san irin cutar da ta barke su 22 sun riga sun mutu.

Malam Shaibu yace tun daga lokacin da su ka san abun dake faruwa kawo yanzu babu wanda ya kara mutuwa. Wadanda suka kamu ma yanzu suna warkewa.

Cutar ta fi kashe dabbobi da dama. Mutanen da suka mutu , dukansu makiyaya ne saboda suna kwana su tashi da dabbobi. Haka kuma mai shan jinin dabbobi idan ya ciji mutum yana iya sa masa cutar. Shan nonon dabba mai dauke da cutar da fidar dabbar dake dauke da cutar, mutum na iya kamuwa da ita.

Malam Shaibu ya kira mutane su dafa nonon dabban da ake kyautata zaton tana dauke da cutar kafin a sha.

Alamomin kamuwa da cutar sun hada da ciwon ciki da zawo da fitar da jinin a kashi ko kuma habo tare da idanu suna yin jawur.

Ga rahoton Souley Barma da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:17 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG