A unguwar Sarkin Adar Gwandu dake cikin birnin Sokoto mutane kimanin dari ukku ne suka kwanta a karamin asibitin dake wurin.
Mazauna unguwar sun bayyana rashin rayuka da dama a unguwar sanadiyar cutar wadda suka dauka tamkar wata annoba. Wata tace rayukan da aka rasa cikin unguwar sun kai hamsin saboda cutar.
Malam Habib Usman yace yanayin zazzabin nada ban tsoro matuka. Da zara mutum ya kamu da cutar koina a jikinsa sai ya dauki ciwo.Wasu kafin a kaisu asibiti rai yayi halinsa.
A lissafin gwamnati mutane biyar ne suka rasa rayukansu sanadiyar cutar amma gwamnatin tace tana daukan matakan gaggawa domin shawo kan cutar.
Dr Balarabe Shehu Kakale kwamishanan kiwon lafiya na jihar yace da jin labarin barkewar cutar suka dauki matakai shida na taimakawa wadanda suka kamu da cutar
Ga rahoton Murtala Faruk Sanyinna.