Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

COVID-19: Habasha Zata Saki Fursunoni 4,000


Kasar Habasha za ta fara sakin fursunoni sama da 4,000 yau alhamis a wani yunkuri na dakile yaduwar cutar coronavirus.

Babban Lauyan kasar Habasha Adanech Abebe, ya ce fursunonin da za’a saki sun hada da wadanda aka yanke wa hukunci kan kananan laifuka, da kuma wadanda ke da kasa da shekara guda da ya rage masu a zaman kaso, tare da matan da ke da jarirai.

Kasar ta Habasha zata kuma tura wasu fursunoni ‘yan kasashen waje wanda aka rike su bisa tuhumar shigowa da miyagun kwayoyi, zuwa kasashensu na asali.

Ya zuwa yanzu, Habasha ta tabbatar da cewa mutum 12 ne suka kamu da cutar coronavirus, amma cutar na ci gaba da yaduwa da sauri a fadin nahiyar Afirka. Gwamnatin ta yanke shawarar daukar matakin ne don yakar yaduwar kwayar cutar.

A halin da ake ciki kuma, Firayim Minista Abiy Ahmed ya yi kira ga 'yan kasar da su rinka ba junansu tazara, ko da yake mutane na yin watsi da gargadin kuma suna ci gaba da yin cinkoso a tarurruka a babban birnin, Addis Ababa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG