NCDC dai ta bayyana hakan ne a shafinta na yanar gizo a safiyar Alhamis, inda rahotani suka yi nuni da cewa adadin mutane 393 da aka samu sun kamu da cutar a jihar Legas a ranar Talata na dga cikin jumlar mutum 1,149 da cibiyar ta fitar a yau.
A yanzu haka dai jumlar wadanda suka kamu da cutar ya kai 184,593.
A cewar NCDC yawan karin da ake samu ya biyo bayan barkewar sabuwar nau’in cutar na Delta da kuma karancin zuwa karbar allurar rigakafi da ake fama da shi a kasar.
Kazalika Cibiyar ta ce a yanzu haka adadin mutanen da ke dauke da cutar a Najeriya ya kai 14,619 karin ga mutun 13,756 a ranar Talata, ko da yake daga cikin su hukumar lafiya ba ta bayyana kashi nawa ne na wadanda ke dauke da sabon nau’in cutar na Delta ba, amma ta ce jihohi 15 ne ciki har da babbar birnin tarrayar kasar Abuja aka sami wannan adadin
Jihar Lagas itace ke kan gaba da mutun 680, sai jihar Ribas dake biye da ita da mutum 157, jihar Akwa ibom da mutum 94, jihar Oyo 56, Edo 36, babban birnin tarayya da mutum 34, yayin da jihar Ogun ke da Mutum 31.
Jihar Ekiti na da mutum 20, jihohin Abia, Nasarawa da Osun na da mutum biyar- biyar, Cross Ribas na da mutun hudu yayin da Jihar Pilato ke da mutum uku, jihar Sokoto na da mutum biyu jihar Kano mutum daya.
Yayin da Gwamnatin Najeriyata amshi sabin nau’ikan allurar rigakafin cutar Covid-19, ta na ci gaba da kira ga al’ummar kasar da su yi allurar la’akari da cewa ita ce hanya mafi sauki ta takaita yaduwar cutar yayin da suke gudanar da ayyukansu na yau da kullum.
A Najeriya an yi nasarar warkar da mutum dubu 167,738 wadanda suka kamu da cutar